Ma’aikatan da ba a tantance ba abin ya shafa.

Gwamnatin jihar Abia ta ce dukkanin ma’aikatan da ba a tantance ba ba za su samu albashin watan Nuwamba ba.
Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu a jihar Prince Okey Kanu ne ya bayyanawa ƴan jarida haka a ranar Litinin.

Wannan mataki na daga cikin batun da majalisar zartarwa a jihar za ta duba a zaman da za ta yi

Kwamishinan ya ce an fara tantance ma’aikatan ne a watan Yuli amma duk da haka akwai waɗanda ba a tantance ba.
Ya ƙara da cewa gwamnatin ta ɗauki matakin dakatar da albashin nasu ne domin gaza cika umarninta.
Kuma sun dauki matakin tantace ma’aikatan ne don ware bara gurbi da kuma waɗanda aka yi cushensu a cikin aiki