Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya aikewa da majalisar dattawan ƙasar sunayen mutane 19 da yaake son nadawa a matsayin kwamishinoni a hukumar ƙidaya ta kasa NPC.

Shugaban ya zabo mutanen daga jihohi 19 na Arewa da kudancin Najeriya.
Jihohin da aka zabo mutanen sun haɗa da Kano, Adamawa, Gombe, Kaduna da jihar Filato.

Sauran su ne Anambra, Borno, Cross River, Enugu, Edo, Imo, Kogi da jihar Ogun.

Sannna an zabo mutum guda a jihohin Taraba, Rivers, Abia, Ebonyi, Delta da jihar Ondo.
Sannna shugaban ya aaikewa da sunayen mutane uku da yake son nadawa a matsayin kwamishinoni na shiyyar arewa maso yamma, kudu maso kudu da kuma kudu maso yamma.