Kotun kolin Najeriya ta yi watsi da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara wanda ya bada umarnin a saki jagoran ƙungiyar ƴan aware IPOB, Nnamdi Kanu.

A cewar kotun ƙoli ta ce tabbas an saɓa doka wajen tasa keyar Kanu daga Kenya zuwa Najeriya bayan ya tsallake sharuɗɗan beli amma hakan ba zata faru ba da ace bai gudu ba.
Bisa haka kotun mai daraja ta ɗaya a Najeriya ta jingine hukuncin bada belinsa, kana ta amince a ci gaba da tuhumar Kanu kan ƙarar zargin hannu a ayyukan ta’addanci.

Tun da farko, Gwamnatin tarayya ta bukaci kotun da ta yi watsi da hukuncin kotun daukaka kara, wadda ta kori zargin cin amanar kasa da ake yi wa shugaban kungiyar IPOB.

Sai dai Lauyan gwamnati, Tijani Gazali, ya roƙi kotun koli da ta tabbatar da hukuncin babbar kotun tarayya, wacce ta yanke cewa dole Kanu ya fuskanci shari’a kan tuhumar da ake masa.