Wata babbar kotun Tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja, ta dakatar da hukumar zabe ta kasa INEC kan sake zaben ‘yan Majalisun Jihar Ribas.

Kotun ta bayar da umarnin ne bayan da ‘yan Majalisu a Jihar guda 27 suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC daga PDP, inda jam’yyar ta PDP ta rushe zaben ‘yan majalisar.
Mai Shari’a, Donatus Okorowo shine ya bayar da umarnin a ranar Lahadi bayan sauya shekar ‘yan Majalisar ne shugaban Majalisar Jihar, Edison Ehie ya bayyana rushe zaben ‘yan Majalisun,tare da bayyana cewa babu kowa akan kujerun ‘yan Majalisun.

Bayan daukar matakin da jam’iyyar ta PDP ta yi kan cewa babu kowa a kujerun,ya sanya ‘yan Majalisar da suka sauya sheka suka shigar da kara gaban kotu bisa matakin da jam’iyyar ta PDP ta dauka a kansu.

A yayin shari’ar Lauyan ‘yan Majalisun Peter Onuh ya bukaci da kotun ta dakatar da hukumar ta INEC da jam’iyyar PDP da Majalisar Jihar kan matakin da suka dauka.
Bayan kammala sauraren korafin masu kara Mai Shari’a Okorowo ya dakatar da hukumar ta INEC akan sake zaben ‘yan Majalisun ,bayan jam’iyyar ta PDP ta rushe zaben.
Alkalin ya kuma dage sauraron karar har zuwa ranar 28 ga watan Disambar shekarar da muke bankwana da ita.
Sauya shekar ‘yan majalisar na zuwa ne a yayin da rikicin siyasa a Jihar ke kara tsananta tsakanin gwamna Fubara da mai gidansa,ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike.