Shugaban kasar Burundi, Evariste Ndayishimiye ya bayyana matakin da ya kamata a rinka dauka kan masu neman maza waɗanda aka fi sani da ‘yan luwadi.

Evariste ya ce kamata ya yi a rinka jefe su da su da masu auren jinsi inda ya ce hakan ba wani laifi ba ne.
Shugaban ya bayyana haka ne yayin ganawa da ‘yan jaridu a ranar Juma’a 29 ga watan Disamba.

Ya ce kasarsa ba ta bukatar duk wani taimako daga kasashen Yamma a kokarin kakaba musu sharadin luwadi da madigo.

Har ila yau, shugaban ya ja aya a cikin littafin Inijla inda ya ce Ubagiji ya haramta neman jinsi kwata-kwata.
Ndayashimiye ya kara da cewa kasarsa bata bukatar fara tattauna magana kan ‘yan luwadi da masu auren jinsi.
Ya ce luwadi da madigo hanya ce a bayyane tsakanin hanyar gaskiya ta ubangiji da kuma hanyar bata ta shaidan.
Burundi na daga cikin kasashen Afirka da suka haramta luwadi wanda hakan ya sa aka sanya hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari.