Anyi kira ga mata da su shiga sana’ar daukar hoto domin yiwa ‘yan uwansu mata a yayin gudanar da wasu tarukan mata zallah.

 

kiran ya fito ne daga bakin Malam Ali Rabi’u Ali Dady a gurin bikin cikar matashiya TV shekaru Bakwai da kafuwa.

 

Malam Ali ya ce shigar mata cikin sana’ar daukar hoto zai taimaka matuka wajen yiwa ‘yan uwansu mata horo a wuraren biki, da sauuran taruukan da su a shafi mata zalla.

 

Malam Ali ya kara da cewa shigar mata cikin sana’ar zai taimaka musu a cikin rayuwa.

 

Sannan yayi kira ga matasa akan muhimmacin dogaro da kai wanda hakan ka iya kai mutum wani mataki na daban a cikin rayuwarsa.

 

Daga karshe ya bayyana cewa dogaro da kai na hana mutum jiran sai anyi masa wata hidima ko zuubar da mutuncinsa

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: