Shugabannin Fulani a jihar Kaduna sun buƙaci hukumar tsaro ta Najeriya ta zakulo wasu sojoji da ake zargi da kisan wasu matasa 17.

An kama tare da hallaka matasan su 17 a Ladduga da ke ƙaramar hukumar Kachia a jihar tsakanin ranar 30 ga watan Disamba da ya gabata zuwa ranar 6 ga watan Janairu da mu ke ciki.
Ƙungiyar Fulani ta ƙaramar hukumar Kachia sun buƙaci babban hafsan tsaron ƙasar da yaa tabbatar an binciko waɗanda su ka aikata haka.

A wani taron manema labarai da su ka gudanar yau, kun ƙungiyar ta zargi sojojin da nuna rashin kwarewa wajen kamawa, tsarewa tare da hallaka mutanen ba tare da bincike ba.

Shugabannin su ka ce daga bisani an zube gawarwakin matasan a kusa da garin, wanda su ka ce hakan tamkar haɗa husuma ne da makoftansu.
Ƙungiyar ta yi kira da kakkausar murya da a tabbatar an zakulo waɗanda su ka aikata kisan domin su fuskanci hukunci.
Idan ba a manta ba, a jihar Kaduna wani jirgin sojin sama ya hallkaa sama da mutane 100 a ƙauyen Tudin Biri yayin da su ke tsaka da mauludi, kuka har yanzu ba a kai ga gabatar da waɗanda su ka aikata hakan ba.