Wasu da ake kyauta zaton ƴan bindiga ne sun hallaka magidanci tare da yin garkuwa da iyalansa.

 

An kashe Tijjani Amedu nai shekaru 53 a duniya sannan aka yi garkuwa da ya’yansa su 13.

 

Lamarin ya faru a Katari da ke jihar Kaduna.

 

Mutanen na kan hanyar dawowa daga tafiya bayan hutun sabuwar shekara kamar yadda makusancinsa ya tabbatarwa da jaridar Punch.

 

Ƴan bindigan sun buƙaci a basu naira miliyan 200 don fansar yaran.

 

Daga bisani an daidaita a kan naira miliyan 50.

 

A ranar Lahadi su ka dakko gawar ɗan uwan nasu tare da binneshi.

 

Sai dai har yanzu ƴaƴan na hannun ƴan bindigan wanda hakan ya sa su ke neman ɗauki daga mahukunta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: