Ƙungiyar manoma kaji sun koka tare da kira ga shugaban ƙasa bisa tsadar abincin kaji.

Ƙungiyar ta ƙasa ta ce matuƙar ba a ɗauki matakin gaggawa ba babu shakka gidajen gona da yawa za su durkushe.


Sakataren ƙungiyar na ƙasa reshen babban birnin tarayya Abuja Hakeem Musa ne ya bayyana haka yau Juma’a a Abuja.
Ya ce a kowanne lokaci su na ci gaba da fuskantar ƙarin farashin kuɗin abincin kajin.
Ya ce hakan babbar barazana ce garesu domin hauhawar farashin gaba yake dada yi.
Ya ce duk da cewar a watan Nuwamba da Disamba ana sa ran samun sauki, amma ba a smau ba ina ga idan aka kai watan Fabrairu zuwa Maris.
Ƙungiyar ta buƙaci shugaban Najeriya da ya duba lamarin don kada a durkusar da kamfanonin baki daya.