Gwamnan Jihar Katsina Umar Dikko Radda ya bai’wa dukkan wani mai rike da mukamin siyasa da ma’aikatan gwamnatin Jihar umarnin bayyanar da kadarorin da suka mallaka a gaban hukumar da’ar ma’aikata ta kasa CCB a Jihar.

Radda ya bayar da umarnin ne a lokacin da ya karbi bakuncin mukaddashin shugaban hukumar Barista Murtala Aliyu Kankia a gidan gwamnatin Jihar.


Gwamnan ya ce yin hakan zai bayynar da gaskiyar kowanne jami’in gwamnati domin kaucewa cin hanci da rashawa.
A cewar gwamnan, gwamnatinsa a shirye ta ke da ta samar da kyakkyawan yanayi ga ma’aikatan Jihar.
A cikin kalamansa mukaddashin hukumar ya bayyana cewa dukkan wanda bai bayyana kadarorinsa duka ba a lokacin da aka buƙata gwamnatin tarayya na da ikon ta kwace kadarorin.
Aliyu ya ce dukkan wani ma’aikaci da ya bayyana kadarorin karya, to za a dakatar da shi ne daga kan mukaminsa na tsawon shekaru Goma ko kuma rasa mukamin baki daya.