Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 1 da ke Sakatariyar Audu Bako, ta yanke wa wasu jami’an sa kai biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya.

 

An yanke musu hukuncin ne bayan samunsu da laifin kisan wani matashi dan shekaru 17 mai suna Ahmad Musa a unguwar Sabon Titin Panshekara.

 

Masu laifin sun hada da Emmanuel Korau da Eliesha Ayuba Jarmai da Irimiya Thimothy da Auwalu Jafar da Mustapha Haladu.

 

Ana tuhumar su ne da laifuka biyu na hadin baki da kuma kisan kai, laifukan da suka saba da sashe na 97 da 221 na Kundin manyan laifuka.

 

Sai dai a yayin sauraron shari’ar duk sun musanta aikata laifukan da ake zargin su da shi.

 

Manema labarai sun ruwaito cewa, a yayin sauraron shari’ar ne lauyan mai kara, Barista Lamido Sorondinki ya gabartar wa kotu shaidu biyar.

 

Har ila yau lauyan wadanda ake kara, Barista Ahmad Muhammad ya gabatar wa kotu shaidu shida ciki har da wadanda ake kara.

 

Yayin da take yanke hukunci, Alkaliyar Kotun kuma Babbar Jojin Jihar Kano, Mai Shari’a Dije Abdu Aboki ta bayyana cewa kotun ta gamsu da hujjojin da mai kara ya gabartar wa kotu, wanda ta yi amfani da su wajen yanke hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: