Kotun koli ta tabbatar da zaben gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara da gwamnan Sokoto Ahmed Aliyu tare da Kefas Agbu a matsayin gwamnan jihar Taraba.

 

Hukuncin da kotun ƙolin ta yanke mai alkalai biyar ƙarƙashin mai shari’a Ibrahim Saulawa ya karanta a yau Alhamis ta yi watsi da daukaka karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Tonye Cole ya yi kan rashin cancantar gwamnan Jihar Rives.

 

Hukuncin daukaka karar jihar Taraba da mai shari’a Mohammed Lawal Garba ya karanta ya kuma yi watsi da karar da jam’iyyar NNPP da dan takararta na gwamna Yahaya Sani suka shigar na shigar da karar da bai cika ba.

 

Kotun kolin ta kuma yanke hukunci kan karar da aka shigar a jihar Sokoto.

 

A hukuncin da Kotun ta yanke wanda Mai shari’a Tijani Abubakar ya karanta ya yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna Saidu Umar suka shigar.

 

Kotun ƙoli da ke Abuja ta yanke na cewa jam’iyyar PDP ta kasa tabbatar da zargin tafka magudi da rashin bin dokar zabe ta 2022.

Leave a Reply

%d bloggers like this: