Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi martani game da jita-jitar yarjejeniya da jam’iyyar APC.

Abba Kabir ya musanta kulla wata yarjejeniya da Shugaba Tinubu kafin yanke hukuncin Kotun Koli a ranar 12 ga watan Janairu.


Yayin da ya ke martani kan wasu takardu da ke yawo a kafafen sadarwa, kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya yi fatali da hakan.
Bature ya ce kawai an kirkire su ne don cimma wani buri amma babu kamshin gaskiya ko kadan tattare da takardun.
Har ila yau, Sanusi ya karyata cewa a cikin yarjejeniyar wai akwai dakatar da rusau da kuma maganar masaurautu da aka kirkira.
Gwamnan har ila yau, ya godewa Shugaba Tinubu da kokarinsa wurin tabbatar da barin shari’a ta yi aikinta yayin hukuncin.
Sannan ya ce babu wani abu da zai hana shi ayyukan aikairi kamar yadda ya ke yi da zai inganta al’ummar jihar Kano.