Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya ce Najeriya ba zata taɓa samun ci gaba ba matuƙar ƴan kasa ba su bin doka da oda.

Zulum ya yi wannan furucin ne a wajen rufe taron lakcar tunawa da Sir Ahmadu Bello karo na 10 wanda aka yi a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, ranar Asabar.


Gwamnan ya kuma lura cewa kasar nan ba za ta daidaita ba idan har cin hanci da rashawa ya ci gaba da yaduwa.
Farfesa Zulum ya kara da cewa ya zama wajibi shugabanni da mabiyansu su haɗu wuri guda wajen bin dokoki da ka’idoji a harkokinsu na yau da kullum.
Ya ce gwamnatinsa na ƙoƙarin samar da shugabanci na gari ta hanyar mai da hankali kan tsaro, aiwatar da muhimman ayyuka, cika alkawuran kamfe, da kara wa ‘yan kasa karfin gwiwa.