Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da wata mata da ƴaƴanta uku a jihar Kaduna.

 

Kamar yadda aka bayyana yan bindigar sun sace mata da ƴaƴanta uku a yayin da suke gida.

 

Lamarin ya faru ne a jiya Litinin da misalin karfe 12 na dare a kauyen Kidandan a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

 

Mai garin Kidandan ya bayyanawa jaridar Daily Trust cewa yan bindigar sun so su sace mijin matar amma yayi musu tirjiya sai suka tafi da iyalansa.

 

Sannan wani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce yan bindigar sun je da yawansu tare da harbi inda suka tsorata mutane sannan suka farma gidan mutumin.

 

Sannan ya ce tuni aka garzaya da mutumin asibiti don duba raunukan da ya samu a lokacin.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: