Shugaban ƙungiyar gwamnonin jihohin arewacin kasa Najeriya Dakta Umar Dikko Radda ya bayyana cewa babu sulhu tsakanin su da yan bindiga.

Gwamnan jihar Katsina kuma shugaban kungiyar gwamnonin jihohin arewacin Najeriya Umar Radda ya bayyana haka ne a yayin da ake ƙaddamar da jami’an CPG wadanda za su yi yaki da yan ta’adda a yankunan.


Radda ya ce sun kaddamar da wannan hukuma ne sakamakon irin yadda ake Kara samun aikin ta’addanci a yankunan.
Ya ce yanzu ba suna magana ne ta nuna bangaren ci a ciki ballantana bambamcin jam’iyya ba.
Suna yin haka ne domin kawowa alumma mafita a jihohi.
Ya ce wannan jami’an CPG da aka horar 2600 za su bayar da gudunmawa yadda yakamata Kuma har ta kai ga kawo karshen yan bindiga.
Sannan ya ce yana fatan kamar yadda Zamfara da Katsina suka yi sauran su biyo baya.
An gudanar da taron ne a babban birnin Zamfara wato Gusau inda gwamnonin Sakkwato Kano, Katsina, Jigawa, Kaduna da Kebbi suka halatta.