Akalla mutane 12 ne suka rasa rayukansu sakamakon wata nakiya da ta fashe da su a jihar Borno.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito ta ce maharan ne da ake zargin yan ta’addan Boko Haram ne suka dasa a kusa da iyaka da ƙasar Kamaru.


An rawaito cewa nakiya yan Boko Haram ce ake zargin sun binne a kusa da kauyen Pulka a jihar Borno.
Mutanen da suka mutu suna kan hanyarsu ta dawowa daga Saran ice a cikin mota iftilain ya faru.
Sannan nakiyar da suka binne mutane 12 ake zargin sun rasu.
Kuma mutane tara ne suka samu raunuka Inda aka Kai su zuwa babban birnin Maiduguri.
A ƴan kwanakin dai ana ci gaba da samun yawan fashewar nakiya ya waɗanda ake zargin yan ta’adda sun binne sakamakon sojoji da Kuma fararen hula.
Sai dai jami’an yan sanda ba su yi magana ba akan hakan tun bayan faruwar lamarin.
