Lauyan da ke kare malamin addinin musuluci  Dakta Idris Dutsen Tanshi ya bayyana cewa da gangan kotu ta sanyawa  wasu sharuda don a kama shi saboda ba za su iya cikawa.

 

Babban lauyan malamin Ahmad Musa ne ya bayyana haka ga manema labarai.

 

Da yake Magana da manema labaran, Musa ya ce wasu Sharruɗan da kotu ta sanya, ba za su iya cikawa ba.

 

Lauyan ya ci gaba da cewa mai shari a Hussaini ya bayar da umarnin kama Dakta a cikin makon da mu ka yi bankwana da shi alhali kuwa an daukaka ƙara wanda hakan sabawa doka ne.

 

Lauyan ya ce bayan da kotu ta bayar da umarni sai aka tura jami’an yan sanda da sojoji da na hukumar kare fararen hula NSCDC kimanin 250 zuwa gidan malamin.

 

Sai dai ba su same shi ba.

 

kafin tafiyar malamin sai da ya bayyana cewa zai yi hijra amma ba guduwa zai yi ba.

 

Har yanzu  jama a  da dama suna bayyana cewa akwai sanya hannun gwamantin jihar Bauchi wajen kama malamin.

 

Sai dai ko a jiya Alhamis sai da gwamantin ta musanta sa hannunta a cikin lamarin na Dakta Idiris Dutsen tanshi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: