Wata kotu da ke babban birnin tarayya Abuja ta wanke Tsohon hafsin Sojin sama daga tuhumar kudi kimanin naira Biliyan 21.5.

 

Alkalin kotun Aneke ne ya yanke hukuncin a yau Talata bayan zaman da aka gudanar bisa zargin.

 

Alkalin ya bayyana cewa tsohon hafsin Sojin sama vice air marshal Adedola Amesun ba shi da alaka da wadannan kudin da ake tuhumarsa.

 

Sannan alkalin Aneke ya ce ya kamata a fara gudanar da bincike akan tsohon hafsin tun suna kan aiki.

 

Sai dai yanzu haka ya wanke shi daga dukkan wata tuhuma da ake Masa akan sace kudin.

 

A kwanakin baya ne dai hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa barna EFCC ta gurfanar da shi a gaban kotu bayan da take zarginsa hadi da wasu mutane da wawure kudade har kimanin naira Biliyan 21.5.

 

Sai dai EFCC ta gurfanar da su a gaban kuliya inda ta wanke su daga zargin.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: