Bayan mako guda da sace yan kai amarya 53 yan bindiga sun kalubalaci dukkan wanda zai iya kubutar da su a jihar katsina.

Wani faifan bidiyo da yake yawo a kafar sadarwa ya nuna yadda yan bindigan suke nuni ga wadanda suka yi garkuwan.

Cikin faifan bidiyon da yake yawo an hangi yadda yan bindigan suka rataya musu bindigu a wuya.

Sannan yan bindigan sun ce dukkan wanda yake ganin zai iya ceton su ya zo.

Sannan sun ce dole sai an biya su kudin fansa kafin su saki yan kai amaryar.

A makon da ya gabata ne wasu da ake zargin yan bindiga ne suka yi garkuwa da mutane su 53 wadanda ke kan hanyarsu ta kai amarya tare da nufar daji da su.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: