Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarni ga dukkan al’ummar kasa Najeriya da su dinga karanta taken Najeriya a duk inda za a gudanar da taro.

Shugaban Najeriya Tinubu ne ya ce duk lokacin da za a yi wani taro na gwamnati da ma sauran alumma a karanta taken Najeriya.


Mai tamakawa shugaban a bangaren harkokin yada labarai Ajuri Nglale ne ya bayyana haka a jiya Alhamis.
Shugaban ya ce ya bayar da umarnin ne domin kasancewar taken Najeriya yana fadawa yan kasar wasu alkawari da biyayya ga kasa da kuma kishin ta.
Bola Ahmad Tinubu ya ce ya wajabta a karanto taken Najeriya zai juyawa da yawa daga cikin yan kasa tunani domin su yi biyayya da kuma kishi tare da dabbaka al’adun kasar.
Wannan na zuwa ne a yayin da abubuwa a kasar ke zama koma baya a idon duniya.
Sannan ake ci gaba da shiga matsin da kunchi daga bangarori da dama