Hukumar hana fasa kwauri ta kasa Kwastom ta sake kama wasu manyan motoci kirar tirela dauke da kayan abinci da ake yunkurin ficewa da shi daga Jihar Legas zuwa ketare.

Kwamandan hukumar a Jihar Timi Bomodi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
Timi ya ce motar da aka kama na dauke ne da buhunhunan wake 400 wanda kudinsu ya kai naira miliyan 61.

Hukumar ta kara da cewa kayan da ta sake kamawa za ta ci gaba da rabawa al’ummar kasar domin fita daga cikin halin yunwa da ake fama dashi a Kasar.

Hukumar ta bayyana cewa kayan abincin da ta ke kamawa ana fita da su ne ba bisa ka’ida, duba da yadda itama kasar ke son abinci ya wadata ga ‘yan Kasar.
Timi ya ce bayan kama kayan sun ajiye a runbunan ajiyar abinci na gwamnati kafin fara rabawa ‘yan Najeriya.
Ko da a makwannin da suka gabata sai da hukumar ta kama wasu motoci cike da buhunhunan shinkafa da aka yi yunkurin ketarawa da su ketare, kuma bayan kama motocin hukumar za ta fara sayarwa da ‘yan kasar domin fitar dasu daga cikin halin yunwa da suke ciki.