Mayakan boko haram a Jihar Borno sun sace ‘yan gudun hijira 319 a lokacin da suka tafi yin itace cikin daji.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa An sace ‘yan gudun hijirar ne a kauyen Ngala da ke karamar hukumar Gambarou Ngala a Jihar.
Wata majiya daga sansanin na ‘yan gudun hijira a Jihar ta bayyana cewa ‘yan ta’addan sun sace matan ne a ranar Lahadin da ta gabata, a yayin dibar itacen domin yin amfani da shi.

Majiyar ta kara da cewa bayan mayakan na boko haram sun yi wa dajin kawanya, inda suka tsere da ‘yan matan suka bar tsofaffin cikinsu.

Bayan tserewa da matan, uku daga cikinsu sun gudu a lokacin da ‘yan ta’addan ke bacci, inda suka shaidawa ‘yan uwansu cewa mayakan boko haram ne suka sace su, kuma su ka kaisu wani daji da ke kusa da kauyen Bukar-Mairam da’da ke Kasar Chadi.
Wadanda suka tsere sun bayyana cewa sai da suka yi tafiyar kwanaki biyu kafin su kawo garin na Ngala.
Wata majiya daga Jami’an tsaro ta bayyana cewa ba tun yanzu ba an hana ‘yan gudun hijirar shiga cikin dazuka domin kaucewa afkuwar hakan.
Sace ‘yan gudun hijirar na daya daga cikin manyan sace-sace da aka yi a Jihar Borno, tun bayan sace ‘yan matan makarantar sakandiren Chibok 276 tun a shekarar 2014 da ta gabata.
