Fitaccen malamin addinin musulunci a Najeriya Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin yin kuskure wajen ceto daliban makarantar kuriga 287 da aka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna.

Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne ta cikin wani shiri na gidan Talabijin na Arise TV a birnin tarayya Abuja.


Gumi ya ce kuskure ne yin amfani da karfin iko gurin ceto daliban daga hannun ‘yan bindiga, kamar yadda gwamnati ta bai’wa jami’an tsaro umarnin kubutar da daliban.
Malamin ya kara da cewa bai kamata gwamnatin tarayya ta bai’wa jami’an tsaro umarnin kubutar da daliban ba da karfin ikonta domin hakan zai kasance matsala garesu.
Gumi ya ce yin sulhu da maharan ne kadai zai kawo karshen duk wani ta’addanci da suke aikatawa a Kasar.
Sannan Malamin ya bukaci gwamnatin da ta samar da wani shirin yin yafiya ga maharan domin kawo karshen su a fadin Kasar.
Malamin ya ce bayan yin afuwa ga maharan, a samar da hanyoyin ilmantar da su domin samar musu da kyakkyawar rayuwa.