Da safiyar yau Asabar wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun kai hari Kauyen Dogon-Noma da ke cikin karamar hukumar Kajuru a Jihar Kaduna.

Wani tsohon shugaban karamar hukumar Cafra Caino ya tabbatarwa da manema labarai faruwar lamarin.


Shugaban ya ce ‘yan ta’addan sun kai harin ne da misalin karfe 5:45am na safe, inda zuwansu ke da wuya suka fara budewa mazauna yankin wuta.
Shugaban yankin ya kara da cewa ya zuwa yanzu ba su san adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba a harin,d uba da yadda wasu daga cikin mutanen yankin sun tsere.
Harin na ‘yan ta’addan na zuwa ne kwanaki uku bayan da wasu ‘yan bindiga suka hallaka mutum guda, tare da yin garkuwa da wasu mata Takwas a kauyen Banono da ke Cikin karamar Hukumar.