Rundunar ‘yan sandan Jihar Akwa-Ibom ta kama wadda ta yi garkuwa da kanta tare da hadin bakin saurayinta a Jihar.

Rundunar ta kuma ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su wata daya da ya wuce.

Jaridar Punch ta rawaito cewa Jami’an sun kuma kama mutane 52 wadanda suke aikata laifuka daban-daban na Jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Waheed Ayilara ne ya bayyana hakan a jiya Juma’a a yayin ganawa da manema labarai.

Kwamishinan ya ce mutane 52 da aka kama an kama su ne da aikata laifin kisan kai, garkuwa da mutane, fashi da makami, damfara, safarar yara da dai sauransu.

Kwamshinan ya kara da cewa budurwar da aka kama ta yi garkuwa da kanta da hadin bakin saurayinta da wasu mutane uku tare da neman kudin fansa naira miliyan hudu a gurin ‘yar uwarta da ke Kasar waje.

Kwamishina ya ce sai dai bayan tsananta bincike jami’an ‘yan sanda suka kamata.

Daga karshe kwamishinan ya ce bayan sun kammala bincike za a gurfanar da dukkan wadanda aka kama a gaban kotu domin yi musu hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: