Gwamnatin jihar Ogun za ta fara siyarwa da ƴan jihar shinkafa tare da yin rahin kashi hamsin na kuɗin da ake siyar da ita a kasuwa.

 

Gwamnan jihar Prince Dapo Abiodun ne ya samar da haka, ya ce gwamnatinsa za ta yi hakan ne domin rage raɗaɗin matsin tattalin arziƙi da akee fama a jihar.

 

Gwamnan ya ceza a fara siyarwa da ma’aikatan gwamnatin jihar shinkafar a farashi mai rahusa, domin sauƙaƙa musu kan halin da ake ciki.

 

Gwamnan wanda ya yi bayanin yayin buɗe bakin azumi ranar Talata, ya ce dukkanin ma’aikatan gwamnatin jihar za su samu shinkafar a wannan farashi.

 

Tuni aka kafa kwamitin da zai kula da harkokin siyar da shinkafar ga ma’aikatan.

 

Sannan an gwamnatin za ta fara da siyarwa da ma’aikata ne daga bisani a kai ga sauran mutanen ƴan asalin jihar.

 

Kuma an ɗauki matakin yin rangwamen ne domin ɗorewa da cigaba da siyarwa mutanen jihar a farashi.

 

A cewar gwamnan, idan aka ce za a raba abincin kyauta lamarin ba zai ɗore ba.

 

Sai dai gwamnan ya ce za a baiwa talakawa da tsofaffi da ba za su iya siya ba shinkafar kyau

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: