Helkwatar tsaro a Najeriya ta fitar da fuskokin mutane Takwas da ta ke nema ruwa a jallo bayan zargin kashe sojoji 17 a jihar Dekta.

 

Hakan na zuwa ne bayan da aka yi jana’izar mutane 17 sojoji da aka yi wa kisan gilla yayin da su ka je domin aikin wanzar da zaman lafiya.

 

An fitar da hotunan fuskoki da sunayen mutane takwas ɗin ne a yau Alhamis.

 

Mutane takwas ɗin cikinsu akwaai maza bakwai sai wata mace guda.

 

Su ne mutane da ake zargi da kashe sojojin Najeirya17 a jihar Delta.

 

Yayin da yake ƴi wa manema labarai ƙarin haske yau, Edward Buba mai magana da yawun helkwatar tsaro a Najeriya, ya yi kira ga ƴan ƙasar musamman mutanen jihar Delta da su ba su haɗin kai tare da kai duk wani bayanin yadda za a kamasu.

 

Sannan jami’an soji za su ci gaba da kai sumame don ganin an tsamo mutanen da ake nema.

 

Bayan kisan gillar da aka yi wa sojojin, an hango wani matashi a wani bidiyo ya na iƙirarin jagoranci da hannu a kashe sojojin.

 

Tuni shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarni don tabbatar da kamo waɗanda ke da hannu a ciki.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: