Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar hallaka wani ɗan bindiga mai suna Junaidu Fasagora tare da wasu da ke ƙarƙashinsa.

A wata sanarwa da sojin su ka fitar jiya Laraba, sun ce aun kashe Junaidu da wasu ƴan bindoga cikin tawagarsa a jihar Zamfara.


An yi musayar wuta da sojin a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
A sanarwar, jami’an sojin sun ce Junaidu da su ka kaahe na da hannu a hare-haren da ake kaiwa shiyyar arewa maso yammacin Najeriya.
Haka kuma ya ƙaddamar da wasu munanan hare-hare a yankunan daga ciki har da garkuwa da mutane.
Jami’an sun ce za su ci gaba da aiki tuƙuru har sai an kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci a Najeriya.
