Wani jami’in ɗan sanda guda ya rasa ransa a sakamakon harin da ƴan bindiga su ka kai shingen bincike a jihar Ebonyi.

 

 

 

 

 

Duk da babu cikakken bayani dangane da jami’an da ya mutu, mai magana da yawun yan sanda a jihar Joshua Ukandu ya tabbatar da faruwar lamarin.

 

 

 

Ya ce ƴan bindigan sun je haye cikin mota sannan su ka kashe jami’in a shingen bincike da ke Ishieke da ke kan titin tsakanin Enugu zuwa Abakaliki a ƙaramar hukumar Ebonyi.

 

 

 

Ya kara da cewa lamarin ya faru a safiyar yau Alhamis kuma zuwansu ke da wuya su ka buɗewa jami’an wuta.

 

 

 

Sai dai bayan faruwar hakaa, kwamishinan ƴan sanda a jihar ya bayar daa umarnin aike daa jami’an zuwa wajen da lamarin ya faru.

 

 

 

Sa’annan ya bayar da umarnin binciko waɗanda su ka aikata haka don tabbatar da sun fuskanci hukunci.

 

 

 

Sannan ya yi kira ga jama’ar da ke jihar da su kwantar da hankalinsu tare da basu bayanai aa kan duk wani abu na zargi ko wanda ba su gamsu da shi ba.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: