Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa babu wata manufa ta siyasa akan shirin binciken tsohon gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.

 

 

 

Gwamna Abba ya bayyan hakan ne a yau Juma’a a lokacin da yake jawabi ga mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayaro a lokacin da sarkin ya kai masa ziyarar gaisuwar Sallah a gidan gwamnatin Jihar.

 

 

 

Abba ya ce dukkan binciken da za a yi akan badakalar kadarorin gwamnatin Jihar hakan ba ya na nufin wata manufa ta siyasa bace sai don tabbatar da gaskiya da kuma samar da hanyar da za a dakile rikicin siyasar da ya faru a baya.

 

 

 

Sannan gwamna Abba ya ce zai yi kokarin ganin an hukunta dukkan masu rura wutar siyasa daga kowacce Jam’iyya a Jihar.

 

 

 

A yayin jawabin sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya jinjina tare da yabawa gwamnan bisa yadda yake gudanar da ayyukan ci gaban al’umar Jihar ta Kano.

 

 

 

Sarkin ya kuma bukaci iyaye a Jihar da su kula da tarbiyyar ‘ya’yansu domin dakile ayyukan daba a Jihar.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: