Majalisar dokokin jihar Rivers ta shigar da korafi ga shugaban ƴan sanda da hukumar tsaron farin kaya ta DSS kan ayyanasu da gwamnan ya yi a matsayin waɗanda babu su.



Hakan ya biyo bayan shirye-shiryen da su ke yi na ganin sun tsige gwamnan jihar Siminilaye Fubara.
A ranar Alhamis gwamnan jihar ya ziyarci majalisar dokokin jihar domin dangane da dambarwar da ke tsakaninsu.
Ƴan majalisar sun zargi gwamnan da shiga majalisar tare da sanin kakakin majalisar ba.
Haka kuma gwamnan ya yi musu karfa karfa a wasu gidajensu da su ke taruwa don ganawa wanda su ka ce babu masaniyar shugaban majalisar ko mataimakinsa.
Guda cikin ƴan majalisar Major Jack ya ce gwamnan ya bayar da umarnin rushe gidajen wanda aka gina shekaru biyu da su ka gabata.
Ƴan majalisar sun shigar da korafin nasu ga shugaban ƴan sada na ƙasa da hukumar DSS wanda su ka ce hakan babar barazanace a garesu.
Jam’iyya APC a jihar ta bukaci majalisar ta gaggauta tsige gwamnan yayin da jam’iyyar hamayya ta PDP a jihar ta buƙaci ƴan majalisar su yi watsi da batun.