Gwamnatin tarayya ta bayyana aniyarta na sake gudanar da zama da ‘yan kungiyar kwadago ta NLC domin sake tattauna akan batun mafi karancin albashin ma’aikatan kasar.

Kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa kan batun mafi karancin albashi ne ya aikewa da kungiyar ta kwadago wata wasika akan sake ganawa da su a ranar Talata mai zuwa.

Shugaban kwamitin Bukar Goni ne ya aikewa da kungiyar wasikar inda ya bukaci shugabannin kungiyoyin NLC da TUC su gayyaci ‘ya’yansu domin sake ganawa da su.

Kwamitin zai sake zama da kungiyar ta kwadago ne bayan kungiyar ta fice daga tattaunawar da su ka fara da kwamitin akan sabon mafi karancin albashi a ranar Larabar da ta gabata.

A ya yi tattaunawar da suka yi a makon da muke bankwana da ni kwamitin ya amince da sake yin gyaran a kan mafi karancin albashin na naira 48,000 inda bayan gbatarwa da kungiyar sabon albashin taki amincewa da shi.

Sai dai kungiyoyin kwadagon na neman gwamnatin tarayya ta amince da naira 615,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan Kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: