Gwamnan Jihar Rivers Siminalayi Fubara ya taya Muhammad Sunusi ll murnar dawowarsa kan kujerar sarkin Kano.

Fubara ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da sakatarensa ya fitar a yau Alhamis.
Gwamnan na rivers ya bayyana cewa yaji dadi dangane da dawo da sunusi kujerar sarkin.

Fubara ya kara da cewa tun daga lokacin da aka cire sunusi a matsayin sarki hakan bai yiwa al’ummar Jihar Kano dadi ba.

Daga karshe Fubara ya jinjinawa gwamna Abba kan amsa kiraye-kirayen al’ummar Jihar da yayi na dawo da sarki.
Inda kuma ya bukaci mazauna jihar da su bai’wa sunusu dukkan goyan baya a domin ganin ya jagorance su cikin aminci.