Rundunar yan sanda a jihar Kaduna ta samu nasarar kubutar da wasu mutane uku bayan da ta kama wani rikakken dan bindiga.

An kama dan bindigan mai shekaru 30, wanda yake a yankin Yan Bokolo da ke Malalin Gabas a karamar hukumar Igabi ta jihar.
Jami’an yan sanda a jihar sun ce an kamashi ne a ranar Talata da misalin karfe 07:00pm na dare.

Mai magana da yawun yan sanda a jihar ASP Mansir Hassan ya bayyana a wata sanarwa da ya aikewa da manema labarai yau JUma’a cewar, bincikensu ya nuna cewa dan bindigan na da alaka da Dogo Halliru wanda rikakken dan bindiga ne da ya addabi jihohin Zamfara, Katsina da Kaduna.

Sanarwar ta ce a ranar Talata, jami’an yan sanda sun yi musayar wuta da yan bindigan a lokacin da su ka tare hanyar Kidandan zuwa Dogon Dawa kuma su ka yi garkuwa da yawa daga cikin mutane.
Sai dai kokarinsu ya sa su ka kubutar da mutane uku daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su.
Kuma sanawar ba ta bayyana adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ba.