Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce an bi dukanin matakan da su ka dace cikin tsari kafin soke dokar karin masarautu a jihar.

Gwamnan na wannan bayani ne a wajen mika takardar kama aiki ga sabon sarkin Kano a karo na biyu Malam Muhammadu Sanusi II.
Ya ce babu wata doka da aka karya wajen bincike da daukar matakin da majalisar ta yi kafin sauya dokar, dalili kenan da ya sa aka yi abin a bude.

Dangane da batun umarnin da kotu ta yi na dakatar da soke dokar sarakuna a jihar, gwamnan ya ce zai yi karar alkalin da ya bayar da umarnin a gaban kungiyar gwamnonin arewa.

Ya ce bayan ganin umarnin, ya yi bincike ya gano alkalin ya na kasar Amerika, kuma ya bayar da umarnin ne da mislain karfe 02:00am na dare.
A cewar gwamnan, ya zama wajibi masu yin doka su ma su bi doka, domin babu wata kotu da take zama da karfe 2am na dare har ta bayar da umarnin.
Sannan ya ce ba za su lamunci ci gaba da irin haka ba wajibi ne su dauki mataki a kai.