Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Imo ta tabbatar da nasarar Hope Uzodinma a matsayin halastaccen gwamnan jihar.

Kotun da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da nasarar Uzodinma a zaman da ta yi yau Juma’a.

Yayin da yake karanto hukuncin, mai shari’a Oluyemi Akintan-Osadebayes ya tabbatar da cewar gwamnan, ya cika ka’idar dokar zabe ta kasa.

Kotun mai alkalai uku, ta yi watsi da karar da Athan Ashonu na jam’iyyar LP ya shigar wanda yake kalubatlantar nasararsa.

A shekarar 2022 hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta ayyana Uzodinma na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Imo da kuri’a 540,308.

Yayin da Samuel Anyanwu na jam’iyyar PDP ya samu kuri’a 71,503, shi kuwa Achonu na jam’iyyar LP ya samu kuri’a 64,081.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: