Wasu mayakan Boko Haram su shida sun mika wuya ga jamian sojin Najeriya a jihar Borno.

Daga cikin mayakan akwai babban kwamandansu wanda shi ma ya ajiye makamansa tare da rungumar zaman lafiya a yankin.
Mai magana da yawun rundunar tsaron hadin gwiwa ta Multinational Joint Task Force MNJTF Abubakar Abdullahi ne ya tabbatar da haka.

Ya ce mutanen sun mika wuyan ne a jiya Alhamis kuma ciki har da Adamu Mohammed wanda ke zama babban kwamanda a cikin kungiyar.

Sannan akwai Hassan Modu ai shekaru 18, sai Nasir Idris mai shekaru 23, da Abubakar Isah mai shekaru 20 sai Abbas Aji mai shekaru 21 da Isah Ali mai shekaru 18.
Kakakin rundunar tsaron ya ce mutanen na tsagen ISWAP wanda su ka stere daga maboyarsu.
Mayakan sun mika wasu makamai da su ke dauke da su, kuma tuni ake ci gaba da bincike a kansu kamar yadda kakakin ya bayyana.