Fiye da mutane 300 ne su ka rasa muhallinsu a sanadin ambaliyar ruwan sama a Ita-Ogbolu da ke karamar hukumar Akure ta Arewa a jihar Ondo.

Gwamnan jihar ya raba tallafi ga mutanen da lamarin ya rutsa da su.
Matamakin gwamnan jihar Olayede Adelami wanda ya wakilci gwamnan ya ce tallafin da aka bayar an yi ne domin rage radadin da ya samesu.

Olayede wanda shi ne shugaban hukumar bayar da agajin gagagwa a jihar, ya ce gwamnan a cirarar da ya kai musu ta karshe, ya yi alkawarin raba kayan tallafi ga wadanda lamarin ya shafa.

Sannan gwamnan ya bayar da umarnin raba tallafin ga wadanda lamarin ya shafa ba tare da duba bangaranci na jam’iyya ba.
Daga cikin kaya da aka raba akwai siminti, karafa da tabarmi.
Al’ummar yankin sun nuna jin dadinsu dangane da tallafin da gwamnan ya raba musu kamar yadda shugaban cigaban yankin Ita-Ogbolu Steve Ojo ya bayyana.