Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayar da takardar kama aiki ga sabon sarkin Kano a karo na biyu Malam Muhammadu Sanusi ll.

Gwamnan ya mika takardar yau Juma’a a fadar gwamnatin Kano bayan da ya sanya hannu a kan sabuwar dokar da ta kafa masarautu a jiya Alhamis.

Injiniya Abba Kabir ya ce sun dawo da tsohuwar dokar da ta kafa masarautun ne tare da dawo da sarki Muhammadu Sanusi ll domin yin adalci ga jama’ar jihar Kano.

Bayar da takardar na zuwa ne kasa da awanni 24 da wata kotun tarayya ta dakatar da soke karin masarautun da majalisar dokokin jihar Kano ta yi.

Batun da gwamnan ke ganin alkalin kotun ya yi hukuncin ba a bisa ka’ida ba.

Tun a ranar Talata majalisar dokokin jihar Kano ta fara yunkurin yin gyaran fuska ga dokar da ta kaa masarautu a Kano.

Idan ba a manta ba, an samu karin sbabin masarautu hudu a jihar a shekarar 2019, wanda aka daga darajarsu zuwa daraja ta daya.

Tun tuni ake zargin gwamntin na shirin rushe masarautun tare da dawo da sarki Muhammadu Sanusi a matsayin sarkin Kano a karo na biyu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: