Gwamnatin Jihar Kano ta yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya fitar da Sarkin Kano Aminu Ado Bayero daga Jihar tunda gwamnatin Jihar ta sauke shi daga kan kujerar sarautar Jihar.

Mataimakin gwamnan Jihar Cormd Aminu Abdulsalam Gwarzo ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a yau Litinin.
Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa kasancewar Aminu Ado Bayero a Jihar hakan na barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’ummar Jihar.

A ganawar da yayi da manema labarai Mataimakin gwamnan ya zargi wasu mutane a cikin jam’iyyar APC da shirya wata zanga-zangar nuna rashin amincewa da rusa masarautun Kano da kuma dawo da Muhammad Sanusi II a matsayin sabon Sarkin Kano.

Gwarzo ya ce zanga-zangar da aka gudanar a Kano wasu ne daga jamiyyar APC suka dauki nauyin zanga-zargar.
Comrd Aminu ya roki Shugaba Tinubu da ya sanya baki akan lamarin domin Jihar ta fita daga cikin halin da ta ke ciki.
Mataimakin gwamnan ya bukaci shugaban kasar da ya dauki matakin gaggawa na fitar da Aminu Ado daga Jihar baki daya wanda zaman a Jihar babbar barazana ce.