Gwamnatin Jihar Kano ta sanar cewa a yau Litinin ta samun umurnin kotun tarayya da ke Jihar na dakatar da rushe masarautun kano tare da tsige sarakunansu Biyar.

Kwamishinan Shari’a na Haruna Isa Dederi ya tabbatar da hakan a yau Litinin tare da tabbatar da karbar umurnin kotun.

Dederi ya bayyana cewa da misalin karfe 10:00am na safiyar wannan rana ne suka samu umurnin kotun akan batun dakatar da nada Sanusi Lamido ll tare kuma tabbatar da Aminu Ado Bayero a matsayin halastaccin sarkin Jihar.

Kwamishinan ya ce da safiyar yau ne wani ma’aikacin kotun ya kawo masa takardar dakatarwar.

Kwamishin ya ce takardar da kotun ta aike musu na dauke da cewa gwamnatin Jihar ta Kano ta dakatar da nada Muhammad Sanusi II a matsayin sarkin Kano na 16 tare da dawo da masarautu biyar din da ta rushe.

Haruna ya kara da cewa takardar tazo musu ne bayan da sun riga sun nada sabon sarki tare da rushe masarautun.

A cewar Dederi bayan samun takardar za su bayyana a gaban kotun tare da mika nasu takardun ga hukuncin da kotun za ta yanke.

Sai dai bayan samun takardar umarnin da gwamnatin kano ta samu a safiyar yau Litinin, da yammacin kuma wannan rana wata babbar kotun Jihar ta dakatar da sarakunan Kano biyar da aka rushe bayyana kansu a matsayin sarakunan Jihar.

Kotun karkashin jagoorancin mai shari’a Amina Aliyu ce ta yanke hukuncin tare da umartar jami’an ‘yan sanda Jihar da su fitar da Sarki Aminu Bayero daga gidan sarautar na Nassarawa.

Sannan Kotun ta kuma dakatar da gwamnatin Jihar daga nada wani sabon sarki a Kano har sai lokacin da ta yanke hukuncin karshe kan karar da aka shigar gabanta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: