Shugaban kasa Bola Tinubu ya mika sakon taya murna ga yaran Najeriya bisa zagayowar ranar yara ta duniya a yau Litinin tare da alkawarin inganta rayuwar yaran Kasar.

Mai magana da yawun shugaban Ajuri Ngelale ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.

A yayin taya yara murnar shugaba Tinubu ya bayyana cewa yara sune tushen ci gaban kowace al’umma duniya.

Tinubu ya ce zai yi iya bakin kokarinsu wajen ganin ya inganta rayuwar yara a Kasar ba tare da wasa da lamarinsu.

Shugaban ya ce zai tabbatar da ganin ilmin ya raya ya habaka a Kasar domin ganin sun zamo al’umma ta gari a fadin Kasar.

A sanarwar da kakakin shugaban ya fitar shugaban ya ce zai yi iya bakin kokarisa wajen ganin ganin yaran Najeriya sun cimma dukkan wani buri nasu da suke son cimmawa a cikin rayuwarsu ta nan gaba.

Shugaban ya kuma taya daukacin iyayen yaran kasar murnar zagayowar ranar tare da bukatar iyayensu da su kula da tarbiyya da kuma koya musu gaskiya da rikon amana.

Shugaban ya ce bai’wa yara nagartacciyar tarbiya hakan ne zai sanya a samu al’umma tagari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: