Rundunar yan sandan jihar Kano ta bukaci shugabannin kafofin yada labarai a jihar da suu ci gaba da bayar da hadin kai kamar yadda su ka saba wajen kawo labaran da za su taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a jihar.

Kwamishinan yan sandan jihar Muhammad Usaini Gumel ne ya yi kiran yayin wata ganawa da yayi da shugabannin kafofin watsa labaran a ofishinsa yau Jumaa.

Gumel ya ce rundunar na yabawa ga yadda yan jarida ke basu hadin kai, sannan ya bukaci hadin kansu da su ci gaba da bayar da goyon baya don dorewar zaman lafiya.

Ya kara da cewa a wannan lokaci da jihar ke fuskantar rikicin masarauta, akwai bukatar kara samun hadin kai ta yadda za a kaucewa hanyar tayar da fitina.

Sannan ya bukaci shuwagabannin da su ci gaba da sa ido a kan ma’aikatansu musamman masu kawo rahotanni doon kaucewa yin amfani da su wajen yada abarai marasa tushe.

An yi taron ne a yau a ofishin kwamishinan yan sanda da ke helkwatar a unguwar Bompai a Kano.

Da dama daga cikin shugabannin kafofin yada labaran ne su ka halarta ciki har da shugaban Matashiya TV Abubakar Murtala Ibrahim

 

A wani cigaban kuma mai martana Alhaji Aminu Ado Bayero ya halarci sallar juma’a a gidan sarki na Nassarawa yayin da sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll ya jagoranci sallar a masallacin gidan sarki na cikin gari.

Wannan na zuwa bayan da rundunar ƴan sandan jihar Kano ta musanta labarin cewa sarakan biyu za su yi sallah a masaccin cikin gari.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Muhammad Usaini Gumel ya ce ba za su bar kowacce kafa da za ta haifar da yamutsi a jihar ba.
An gudanar da sallar juma’a yau wanda kowanne ya yi sallah a masallacin da ya halarta lami lafiya.

Kafin wannan sanarwa daga makusantan Alhaji Aminu Ado Bayero ce ta fara yawo cewar zai jagoranci sallar Juma’a a gidan sarki na cikin gari.

Kuma wani da ya taɓa riƙe sarautar gargajiya kuma makusanci ga sarkin Musa Ilyasu Kwankwaso ya shelanta gayyatar jama’a.

A gefe guda kuwa Sanusi Bature Dawakin Tofa mai magana da yawun gwamnan Kano ya shelanta gayyata a madadin magoya bayan sarki Muhammadu Sanusi ll.

Batun da ya dauki hankalin jami’an tsaro har ta kai ga sun samar da daidaito a kai.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: