Dan takara shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zabi Sanata J.D Vance a matsayin wanda zai masa mataimaki.

Sanata J.D Vance dai na da shekaru 39 a duniya wanda a baya ya kasance mai caccaka da sukar tsarin siyasar Donald Trump.
Sai dai daga baya ya dawo goya masa baya.

Donal Trump na takarar shugaban kasar Amurka ne karkashin jam’iyyar Republican.

A makon jiya ne aka kai hari Pennsylvania yayin da yake gangamin yakin neman zabe.
An bude wuta a wajen sai dai daga baya jami’an tsaro sun kubutar da shi duk da cewar ya ji rauni a fuskarsa da kunnensa.
Donal Trump ya ce an so a hallakashi ne a wajen taron amma Allah ya tseratar da shi.
Tuni shugaban Amurka Joe Biden ya yi Ala Wadai da lamarin.
Ya bukaci yan kasar da su hada kai don tabbatar da zaman lafiya.
Ana sa ran za a yi zaben ne a watan Nuwamban shekarar da mu ke ciki.