Hukumar ta shirya jarabawar kammala makarantun sakandare ta Afrika ta yamma WAEC ta bayyana cewa ta rike sakamakon jarabawar dalibai 215,267 daga cikin akalla dalibai 1,814,344 daga makarantun sakandare 22,229 na fadin Najeriya da suka rubuta jarrabawar.

Hukumar ta bayyana hakan a sanarwar da ta wallafa a shafinta na X a yau Litinin.

Shugaban hukumar a Najeriya Amos Josiah Dangut ya bayyana cewa hukumar ta rike sakamakon daliban ne bisa zarginsu da aikata laifin satar jarabawa a lokacin rubuta jarrabawar.

Acewar hukumar adadin daliban da aka rike sakamakonsu ya ragu da kashi 4.37 daga kashi 16.29 da aka samu a jarabawar ta shekarar 2023 da ta gabata.

Rahotannin sun bayyana cewa adadi ya nuna kashi 11.92 na mutane 1,805,216 da suka rubuta jarrabawar hukumar jarrabawar ta ambata.

Shugaban hukuma a Najeriya ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da daukar mataki akan dukkan wasu laifuffuka da suka shafi magudin jarrabawa.

Shugaban ya ce malamai da dalibai masu dabi’ar magudin jarrabawa suna lalata fannin ilimi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: