Wata babbar kotun jihar Rivers mai zama a garin Fatakwal ta soke matakin tsige zababbun shugabannin jam’iyyar APC na jihar karkashin jagorancin Emeka Beke.

Alkalin kotun Mai shari’a Sika Aprioku ne ya yanke hukuncin a zaman da ya gudanar a yau Litinin.

Ayayin yanke hukuncin Akalin ya ce kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC ta kasa ya yi kuskure a lokacinda ya rushe zababbun shugabannin jihar ba tare da wani dalili ba.

Alkalin ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta Kasa ba ta da wani hurumi na korar zababbun shugabanni na kowace jihar.

Sannan kotu ta ce jam’iyyar ba ta da ikon nada wani kwamitin rikon kwarya gabanin karewar wa’adin zaɓaɓɓun shugabannin jam’iyya.

A don haka ya sanya kotun ta tsige shugaban jam’iyyar ta APC na rikon ƙwarya a Jihar Chief Tony Okocha tare da dukkan mambobin kwamitinsa, daga bisani kuma ta mayar da Emeka.

Alkalin ya kuma haramtawa Tony Okocha da mambobinsa ci gaba da bayyana kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar ta APC a jihar ta Rivers.

Sai dai bayan yanke hukuncin kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar a jihar karkashin Okocha, ya yi fatali da hukuncin da babbar kotun Jihar ta yanke.

Inda kwamitin ya ce nan bada dadewa zai daukaka kara akan batun.

Leave a Reply

%d bloggers like this: