Dan takarar shugaban Kasa a Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Tinubu ba shirya karbar mulkin Kasar.

Atiku ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa kan yada labarai Paul Ibe ya fitar.

Alhaji Atiku ya ce abin kungiya ne yadda gwamnatin Tinubu ta zuba idanu sai da ‘yan Kasar suka fito kan tituna domin nuna mata irin wahalhalun da suke sha na tsadar rayuwa da kuncin talauci.

Dan takarar ya kara da cewa matukar har yanzu jam’iyyar APC mai mulkin Kasar, ba ta gane irin wahalhalun da ‘yan Kasar sha ba, hakan ya nuna cewa tun da fari ba ta shirya yin mulkin ƙasar ba.

Kazalika Alhaji Atiku ya ce tabbas akwai ƙalubale kafin karbar Tinubu mulkin Kasar, daga tsohuwar gwamnatin Muhammad Buhari inda ta yi kura-kurai kafin shudewar ta.

Atiku ya bayyana ce a zamanin Buhari tattalin arzikin kasar ya durƙushe sau biyu, sakamakon ba ta san komai ba akan tattalin arziki ba, da kuma cin hanci da rashawa.

Acewarsa duk kuskuren da Buhari ya tafka a baya Tinubu ya fishi.

Atiku ya kara da cewa ta ya ya farashin kayan abinci zai sauko a kasar sakamakon cewa manoma ba za su iya komawa gonakinsu ba domin yin noma saboda matsalar rashin tsaron da kasar ke fama da ita.

Atiku ya ce abin kunya ne babu wani abu a ƙasa da zai nuna cewa gwamnatin Tinubu ta shirya magance matsalolin al’ummar Kasar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: