Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun hallaka wasu matafiya bakwai akan babbar hanyar Takum zuwa Wukari da ke Jihar Taraba.

Maharan sun hallaka matafiyan ne a safiyar yau Litinin a yankin.
Shaidun gani da ido sun bayyana jaridar Daily Trust cewa ilahirin matafiyan ’yan garin ne, kuma suna kan hanyarsu ne ta zuwa garin Sa’ayi da ke Jihar Benue a lokacin da maharan suka farmusu a tsakanin garin Chanchangi da garin Wukari.

Shima wani shaidan gani da idon ya ce ‘yan bindigan sun budewa motar matafiyan wuta ne, inda kuma duk suka kashe mutanen cikinta amma ba su ɗauki komai ba a cikin motar.

Shaidan ya bayyana cewa ‘yan bindigan na daga cikin ’yan maharan da suka addabi dajikan da ke tsakanin Jihar Benue da Jihar Taraba.
Rahotannin sun kara da cewa a dai hanya ce aka hallaka basaraken garin Chanchangi tare da babban ɗansa a watan Yulin da ya gabata.
Rahotannin sun ce hanyar da maharan ke sharafinsu su na tare mutane tare da yi musu fashi da garkuwa da matafiyan da ke bin hanyar domin karɓar kuɗin fansa.
Da aka tuntuɓi mai magana da yawun ’yan sandan jihar DSP kwach akan lamarin ya bayyana cewa zai yi bincike akan lamarin.