Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso Yamma Salihu Lukman ya bayyana cewa zanga-zangar da aka gudanar a Kasar wata babbar manuniyace ta tsige shugaba Bola Tinubu daga mulkin Kasar.

Lukman ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi.

 

Lukman ya bayyana cewa zanga-zangar da matasan kasar suka yi kan tsada rayuwa ya isa ya zama babbar shaida da za ta sanya a sauke Tinubu daga shugabancin Kasar.

Salihu ya ƙara da cewa zanga-zangar da aka yi ta kai matakin da ya kamata abi doka wajen sauke gwamnoni da dama daga kan kujerunsu.

Lukman ya ce a bayyane ya ke tsarin demukradiyyar Najeriya ba ya aiki kamar jam’iyyun siyasa da kuma ‘yan majalisun tarayya.

Tsohon mataimakin jam’iyyar ya ce abubuwan da ke faruwa a yanzu a Kasar kamata ya yi Tinubu da galibin gwamnonin Kasar sun kama hanyar tsigewa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: